in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mun Gama Shiryawa Domin Buga Wasan Farko Da Crotia, Cewar Kocin Nijeriya
2018-06-13 11:08:03 cri

Mun samu labari daga tashar intanet na Leadership A Yau ta Najeriya da ke cewa, mai koyar da tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, ya tabbatar da cewa 'yan wasansa sun shirya tsaf domin fafata wasan farko na gasar cin kofin duniya da 'yan wasan kasar Croatia.

A kwanan nan dai an samu shakku a kan ko 'yan wasan na Super Eagles za su yi abin arziki a gasar bayan da kungiyar ta buga wasanni uku a jere na sada zumunta amma babu wanda tasamu nasara inda ta yi rashin nasara a wasanni biyu ta buga canjaras a wasa daya. Sai dai mai koyar da 'yan wasan, Gernot Rohr, dan kasar Jamus, ya bayyana cewa ya yarda da 'yan wasansa kuma ya san za su shirya kafin lokacin wasan saboda ya san suna da dabara da juriya kuma sun iya fuskantar wasa duk wahalarsa.

Ya ci gaba da cewa duk da cewa kasar ba ta samu nasara a wasannin share fagen fara gasar ba amma hakan ba ya nufin cewa ba za su yi kokari ba saboda wasan sada zumunta daban sannan kuma gasa daban kuma kowanne wasa da yadda ake buga shi. Ya ci gaba da cewa za su dinga bin wasannin daya bayan daya domin ganin kowanne sun shirya kuma sun yi amfani da damar da suke da ita wajen samun nasara sannan kuma ya ce 'yan wasan suna bukatar goyon baya ga 'yan kasar.

A karshe ya ce a wasannin da suka buga a baya na sada zumunta sun ga irin kura kuren da suka yi kuma za su gyara kafin fara gasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China