in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar mutane 7 a Nijeriya
2018-05-05 15:49:54 cri
Mahara 4, tare da wasu mutane 3, sun mutu sanadiyyar wasu hare-haren kunar bakin wake, da aka kai jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya da sanyin safiyar jiya Juma'a.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, Edet Okon, ya ce wasu mutane 7 kuma sun jikkata, biyo bayan hare-haren da aka kai wasu kauyuka 2 dake kusa da Maiduguri babban birnin jihar.

'Yan kunar bakin waken ciki har da mace guda, sun kai hare-haren ne a wajen dandazon jama'a a kauyukan Mainari Kanuri da Mainari Shuwa.

Ya kara da ecwa, nan take aka tsaurara matakan tsaro a yankin da kuma birnin Maiduguri.

Ana zargin Kungiyar Boko Haram dake muggan ayyukanta a yankin arewa maso gabashin kasar da kai wannan harin.

Ko a ranar Alhamis da ta gabata, 'yan kunar bakin wake sun tada bam dake jikinsu a wani yunkuri na kai hari a wajen birnin Maiduguri, al'amrin da ya yi sanadin mutuwarsu.

Haka zalika a ranar Alhamis, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari wani sansanin soji dake da nisan kilomita 12 daga birnin Maiduguri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China