Jaridar kasar Morocco ta "daily Le Matin" ta rawaito hakan a litinin din nan, tana mai cewa sassan biyu, sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin ne, yayin wani biki da sarki Mohammed na 6, da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari suka jagoranta, da yammacin ranar Lahadi a fadar mulki ta birnin Rabat.