in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na da kyakkyawan fata game da gasar cin kofin duniya, duk rashin tabuka abun kirki a wasanninta na baya-bayan nan
2018-06-08 15:00:43 cri

Duk da rashin tabuka abun a-zo-a-gani yayin wasannin sada zumunta da ta buga da Ingila da Jamhuriyar Czech, Nijeriya na da yakinin za ta kai bantanta a gasar cin kofin duniya ta bana.

Ministan matasa da wasanni na kasar Solomon Dalung, ya bayyana wa manema labarai a birnin Lagos cewa, an buga wasannin sada zumunta ne bisa wasu muhimman tsare-tsare.

Ya ce, asalin bajintar tana ga gasar cin kofin duniya, yana mai cewa idan kuma aka gurgunta abun da aka shiryawa gasar yayin wasannin sada zumunta, ke nan hakarsu ba ta cimma ruwa.

Biyo bayan rashin tabuka abun kirki yayin wasannin sada zumuntar, da yawa daga cikin masoyan kwallon kafa a Nijeriya sun nuna shakku game da tafiyar kungiyar a Rasha.

Ministan ya kara da cewa, duk da shakkun da masoyan kwallon kafar suka nuna, akwai yiwuwar kungiyar ta ba su mamaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China