Gwamnatin Nijeriya, ta yi kira ga bangarori masu zaman kansu, su ci gajiyar kyakkyawan yanayin kasuwanci da ke akwai a kasar, don zuba jari a bangaren raya harkokin wasanni.
Ministan matasa da wasanni na kasar Solomon Dalung ne ya yi kiran jiya a Lagos, cibiyar harkokin kasuwancin kasar, inda ya ce, akwai bukatar bangarori masu zaman kansu a kasar su shiga a dama da su a bangaren, domin gano dimbim damarmakin dake kunshe cikin zuba jari a harkokin wasanni.
Solomon Dalung ya shaida wa manema labarai cewa, bangarori masu zaman kansu ne ke bunkasa harkokin wasanni a duniya, yana mai cewa, ba lallai ne a samu alfanu nan take ba, amma jari ne da idan ya habaka zai shafe lokaci mai tsawo. (Fa'iza Mustapha)