in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi Bikin Makon Arewa a kasar Sin
2018-05-16 19:34:10 cri

An yi bikin Makon Arewa a birnin Shenyang na lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin a daren ranar 12 ga watan Mayu.

Hadaddiyar kungiyar daliban da suka fito daga arewacin Nijeriya, wadanda suke karatu a nan kasar Sin ce ta amshi bakuncin bikin, a kokarin yayata al'adun gargarjiyar kabilu daban daban dake arewacin Nijeriya, da inganta hadin gwiwar dalibai masu karatu a kasar Sin, da kyautata fahimtar juna a tsakanin jama'ar Nijeriya da na Sin.

 

Daliban Nijeriyar dake karatu a wasu biranen Liaoning da kuma abokansu mazauna wurin, da wasu 'yan kasar Sin da ke koyon harshen Hausa, da ma wadanda aikinsu ya shafi harshen Hausa fiye da dari 2 ne suka halarci bikin.

A yayin bikin, daliban Nijeriya da ke karatu a kasar Sin sun yi wake-waken gargajiya na Hausawa, da Fulani, da Kanuri, da Nupe, da Jukun, sun kuma gwada wa 'yan kallo tufafin kabilun, tare da nuna wasannin kwaikwayo cikin harshen Hausa. Hakan ya samar wa 'yan kallo damar kara fahimtar al'adun kabilun Nijeriya.  

Har ila yau kuma, daliban kasar Sin da suke koyon harshen Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, su ma sun nuna wasanni masu halin musamman na haduwar al'adun kasashen Sin da Nijeriya. Wadannan matasan kasar Sin masu sanye da tufafin gargajiyar Nijeriya, sun yi shahararriyar rawar Rariya ta Hausawa, tare da nuna wasan Taiji mai kayatarwa. Sun samu yabo sosai daga 'yan kallo.  

Tun bayan taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka a shekarar 2015 har zuwa yanzu, mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da Afirka tana ta kara kyautata. Masu shirya bikin sun bayyana cewa, yanzu daliban Nijeriya kusan dubu 1 ne suke koyon ilmin likitanci, da kimiyya da fasaha, da tattalin arziki da dai sauransu, a wasu jami'o'i da ke biranen Shenyang, da Jinzhou da sauran biranen lardin na Liaoning. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China