in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar masana'antu da cinikayya ta Lagos dake Nijeriya ta yi kira da hana fitar da katako zuwa kasashen waje
2018-05-21 13:36:21 cri
A kwanakin baya, shugaban kungiyar masana'antu da cinikayya ta Lagos dake tarayyar Nijeriya Babatunde Ruwase, ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta hana fitar da katako zuwa kasashen waje. Ruwase ya bayyana cewa, yanzu haka an yanke bishiyoyi masu tarin yawa, an kuma gurbata yanayin Nijeriya a sakamakon fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da yanke bishiyoyi masu haifar da sauyin yanayi, matakin da ya haddasa fadadar yankunan da hamada ke mamaya, da kuma gurbatar ruwa. Hakan a cewar jami'in ya haifar da illa ga zaman rayuwar jama'ar yankuna da dama na kasar. Ya ce, rikicin manoma da makiyaya a yankin Nijer Delta ma ya barke ne a sakamakon gurbatar yanayi. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China