Shugabannin mambobin kungiyar da suka zo birnin Qingdao don halartar taron sun hada da: firaministan kasar Indiya Narendra Modi da shugaban kasar Kazakhstan Nursutan Nazarbaev da shugaban kasar Kyrgyzstan Sooronbay Zheenbekov da shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain da shugaban Rasha Vladimir Putin, da na Tajikistan Emomali Rakhmonov, da kuma shugaban Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev.
A sa'i daya kuma, shugabannin kasashe 'yan kallo wadanda suka zo sun hada da: shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani da shugaban Belarus Alexandr Lukashenko da na Iran Hassan Rouhani da kuma shugaban kasar Mongoliya Khaltmaa Battulga.
Bugu da kari, wasu wakilan MDD da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa su ma za su halarci taron. (Maryam)