in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: An cimma daidaito kan wasu manufofi a taron koli na kungiyar SCO
2018-04-25 13:21:38 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyanawa 'yan jarida bayan da ya shugabanci taron majalisar ministocin harkokin wajen kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO a birnin Beijing a ranar 24 ga wata cewa, taron ministocin harkokin wajen ya aza tubali, na gudanar da taron koli na kungiyar SCO a watan Yuni a birnin Qingdao. Ya ce bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an tabbatar da wasu manufofin da aka fatan cimmawa a gun taron koli na Qingdao.

Wang Yi ya bayyana cewa, an cimma daidaito kan manufofin a gun taron ministocin harkokin waje da ya gudana. Wadannan manufofi sun hada da na farko, bukatar zurfafa hadin kai da yin imani da juna. Na biyu, a kara yin hadin gwiwar kiyaye tsaro. Na uku, a kara hadin gwiwa wajen gudanar da manufofin samun ci gaba. Na hudu, a inganta hadin gwiwa mai dacewa. Na biyar, a kara yin mu'amalar al'adu. Na shida, a kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China