A gobe Lahadi 10 ga wata, gidan rediyon kasar Sin CRI, zai gabatar da shirye-shirye kai-tsaye kan wasu muhimman ayyuka na taron SCO cikin harsunan Rashanci da Ingilishi da kuma Sinanci.
Har wa yau, za a watsa shirye-shiryen kai-tsaye ne ta tashar Intanet da manhajar wayar salula ta APP, da kuma shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter na CRI cikin harsuna 40, ciki har da Hausa, da Swahili, da Ingilishi, da Larabci, da Rashanci, da Japananci da Farasanci da Jamusanci da sauransu.(Murtala Zhang)