in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika wasikar taya murna ga taron koli karon farko na kafofin yada labarai na SCO
2018-06-01 11:36:06 cri
A yau ne aka bude taron kolin yada labarai na kungiyar SCO karo na farko a birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wasika don taya murnar bude wannan taro.

A cikin wasikar, Mista Xi ya bayyana cewa, yana fatan alheri ga taron kasancewarsa taron kolin kafofin yada labarai kungiyar SCO na farko, kana yana maraba da mahalarta taron daga kafofin yada labarai daban-daban na duniya.

Ya ce, ana kara samun labarai game da halin da duniya ke ciki a halin yanzu, kafofin yada labarai na taimakawa sosai wajen yin mu'ammala tsakanin jama'ar kasashe daban-daban. A shekara daya da ta gabata, Mista Xi ya ba da shawarar kiran irin wannan taro na SCO da zummar ciyar da mu'ammala da tuntubar juna ta fuskar al'adu tsakanin mambobin kungiyar ta SCO.

Shugaba Xi, ya ce ya yi imanin cewa, taron na wannan karo zai ba da gudunmawa mai kyau wajen kara hadin kai tsakanin mambobin SCO.

Mista Xi ya kara da cewa, kafofin yada labarai a matsayin gadar da ke kara hadin gwiwa, mu'ammala da yin musanyar ra'ayi tsakanin al'ummomin mambobin SCO, kamata ya yi su kara kokari wajen yada tunanin Shanghai, sa kaimi ga hadin gwiwa da kara tuntubar jama'a. Sin na nacewa ga ciyar da SCO gaba, kuma tana fatan hada kai da bangarori daban-daban don kafa al'umma mai kyakkyawar makoma a wannan yanki.

A karshe, ya yi fatan taron zai samu nasara da ma kyakkyawan sakamako. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China