A yayin ganawar Xi ya nuna cewa, tun bayan da aka kafa kungiyar SCO, kullum kasashe mambobin suna ba da muhimmancin da batun tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashe mambobin kungiyar don kulla wata sabuwar dangantakar kasa da kasa bisa nuna girmama juna da adalci da samun nasara tare, don samun makomar bai daya ta dan Adam.
Wakilan tawagogin kasashen waje sun yi jawabi cewa, kasashensu na goyon bayan shawarar da kasar Sin ta gabatar a matsayinta na kasar dake shugabantar kungiyar a fannonin tabbatar da ra'ayin bai daya da shugabannin suka cimma, da tinkarar kalubalen da kasashe mambobin kungiyar ke fuskanta, da kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. (Bilkisu)