Kasashe 6 ne suka shiga zaben na wannan karo da aka yi a jiya. Da yake an zabi wakilan wucin gadin ne bisa yankuna daban daban, shi ya sa, kasashen Jamus da jamhuriyyar Dominican da Afirka ta Kudu da Belgium ba su da abokan karawa, yayin da kasashen Indonesia da Maldives suka nemi wakilcin yankin Asiya da Pacific.
Babban taron zauren MDD, ya zabi wakilan wucin gadin kwamitin sulhun ne ta hanyar jefa kuri'un da babu suna, kuma kasashen da suka sami kuri'u sama da kashi 2 bisa 3 ne suka lashe zaben. (Maryam)