in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musayar ilimi ginshiki ne na kawar da fatara da yunwa a duniya, in ji wasu jami'ai
2018-06-06 10:04:01 cri

Wakilai daga kasashe daban daban, da na hukumomin MDD, sun bayyana musayar ilimi da kwarewa, a matsayin ginshikin shawo kan matsalolin fatara da yunwa da ake fuskanta a sassan duniya daban daban.

Mahalarta taron muhawarar da ta gudana a helkwatar asusun kasa da kasa na raya ayyukan gona ko IFAD a takaice, ciki hadda wakilan kasashen Ghana, da Senegal, da Kenya, sun tofa albarkacin bakinsu, game da matakan da suka dace a dauka, domin cimma nasarar kudurori 2 na farko na wanzar da ci gaban karni karkashin shirin SDGs, wato batun yaki da fatara da yunwa, kamar yadda hakan ke kunshe cikin ajandar SDGs din ta nan da shekarar 2030.

Kwararru kimanin 90 ne suka halarci taron na jiya Talata. Kuma kungiyar ba da agajin jin kai ta kasa da kasa reshen kasar Sin ta IPRCC, da cibiyar lura da yanar gizo ta Sin CIIC, da hukumomin MDD na shirin samar da abinci WFP, da ta raya ayyukan gona FAO, da asusun IFAD ne suka dauki nauyin shirya taron. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China