Sanarwar da kakakin Majalisar Farhan Haq ya fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na kira ga dukkan bangarori su kwantar da hankali tare da kauracewa tada fitina, sannan ya bukaci 'yan siyasa da al'umma, su duba yuwar hawa teburin sulhu domin samun kyakkyawan yanayin gudanar da sahihin zabe mai adalci.
Sakatare Janar din ya bayyana takaici game da yadda gwamnati ta haramtawa bangarorin adawa gudanar da zanga-zanga. Ya ce abu ne mai muhimmanci a tattauna don samun maslaha game da rikicin siyasar kasar, yana mai kira ga Gwamnatin ta tabbatar da kare hakkokin dan Adam da 'yancin bayyana ra'ayi. (Fa'iza Msuatpha)