Da yake jawabi a wani taron hadin gwiwa na jami'an ofishoshin kare rariyar Ozone na kasashen Afrika 54 da aka fara jiya Litinin a Gaborone babban birnin Botswana, mataimakin Daraktan Ofishin hukumar kula da muhalli na MDD a Afrika, Frank Turyatunga, ya ce yawan hayaki masu guba da a karshe za a kaucewa sakamakon kauracewa amfani da sinadaran HFC, tare da karin moriya masu dorewa da za a samu, za su dogara ne kan matakan da kasashen za su dauka game da muhimman batutuwa.
Kokarin nahiyar na kaucewa amfani da sinadaran, ya biyo bayan taro na 16 da ministocin kasashen nahiyar suka yi kan muhalli a birnin Kigali, wanda ya amince da gyara yarjejeniyar Montreal, da kasashen duniya suka cimma kan sinadaran dake illa ga rariyar Ozone. (Fa'iza Mustapha)