Kudurin wanda kasashen Cote d'Ivoire, da Kuwait, da Netherlands da Sweden suka gabatar, ya samu amincewar daukacin mambobin kwamitin, ya kuma bukaci kawo karshen amfani da yunwa kan fararen hula, a matsayin wani makami na yaki.
Kudurin ya yi nuni da yadda wasu sassa ke keta hakkokin bil Adama na kasa da kasa ta wannan siga. Yana mai bayyana cewa kaso mafi yawa daga al'ummun dake fuskantar karancin tsaro, da kaso kusan 75 na yara 'yan kasa da shekaru 5 dake fama da karancin abinci, suna rayuwa ne a yankuna dake fama da tashe tashen hankula. Yawan wadannan al'ummu a cewar kudurin na kwamitin tsaro ya kai mutum miliyan 74.
Kudurin ya alakanta karancin abinci da al'ummu da dama ke fuskanta da rigingimu dake aukuwa, yana mai fatan ganin an dauki sahihan matakai, na kawo karshen wannan mummunan yanayi da jama'a da dama ke fuskanta.
Domin cimma wannan buri, kudurin ya ja hankalin dukkanin sassa da ba sa ga maciji da juna a yankuna daban daban, da su rika baiwa fararen hula kariya, ta hanyar kaucewa lalata muhimman wurare, kamar gonaki, da kasuwanni, da wuraren sarrafa abinci, da na samar da ruwa, da rumbunan ajiyar kayan abinci da dai sauran su.(Saminu Alhassan)