in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kira taron tunawa da zartas da yarjejeniyar yakar cin hanci da rashawa
2018-05-24 10:27:28 cri
A jiya Laraba, MDD ta kira taron tunawa da zartas da yarjejeniyar yakar cin hanci da rashawa shekaru 15 da zartas da ita, taron da ya samu halartar wakilai daga kasashe da kungiyoyi 184, wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Shugaban babban taron MDD Miroslav Lajcak, da babban sakataren Majalisar Antonio Guterres, suna cikin mahalarta taron, inda manyan jami'an, suka cimma ra'ayi guda game da amfani da yarjejeniyar wajen kara taka rawar gani, da karfafa huldar hadin kai tsakanin kasashen duniya, da daukar kwararan matakai don magancewa, da kuma yakar cin hanci da rashawa.

Tawagar kasar Sin da ta halarci taron ta jaddada cewa, yaki da cin hanci da rashawa mataki ne na nuna adalci, wanda ya kasance burin bai daya na al'ummomin kasashe daban daban. Yayin da ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban ta fuskar yaki da cin hanci, ya kamata a daina kawar da kai game da duk wani yunkuri na aikata zamba, da kafa wani tsarin aiki wanda zai hana masu aikata rashawa samun tsira, da gudanar da hadin gwiwa ba tare da kafa wani shinge tsakanin al'ummomi ba.

Kasar Sin tana tsayawa kan matsayin da ta dauka, na nuna cikakken goyon baya ga MDD, domin ta taka rawa a matsayin wani muhimmin dandali, inda kasashe daban daban za su samu damar hada kansu wajen yakar cin hanci da rashawa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China