in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a mayar da Rasha cikin kungiyar G7, in ji shugaban Amurka
2018-06-09 16:13:09 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, ya kamata a mayar da kasar Rasha cikin kungiyar G7, inda ita kuma Rashar ta ce a yanzu, ta fi mayar da hankali ne kan sauran harkokin hadin gwiwa.

Da safiyar jiya Jumma'a, kafin tashinsa zuwa kasar Canada don halartar taron kolin kungiyar G7 ne Donald Trump, ya ba da shawarar da a mayar da Rasha cikin kungiyar G7, yana mai cewa, ya kamata a dawo da ita teburin shawarwari.

Dangane da wannan shawara ne kuma, babban sakataren ofishin yada labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya ce, kasarsa ta fi mai da hankali ne kan sauran harkokin hadin gwiwa. Inda shi kuma shugaban kwamitin yada labarai na kwamitin tarayyar kasar, ya bayyana kungiyar G7 a matsayin maras amfani, yana mai cewa, wannan batu bai zai ja hankalin kasar kamar yadda ya taba yi a baya ba.

Firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte, ya nuna amincewa da shawarar da Donald Trump ya bayar, inda yake ganin mayar da Rasha zai tallafawa bangarorin kungiyar. Sai dai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Canada ya ce, kasarsa ba ta amince da wannan shawara ba.

A nata bangaren kuma, shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa, a halin yanzu, bai dace a mayar da Rasha kungiyar ba, tana mai cewa kasarta za ta yi shawara da Rasha kan batun yadda ya kamata.

A jiya Jumma'a ne aka bude taron kolin kungiyar G7 a garin Chara na lardin Quebec dake kasar Canada. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China