Babban sakataren ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa a yayin bikin mika kujerar shugabancin kungiyar G77, wanda aka shirya a yammacin jiya Juma'a a hedkwatar MDD dake birnin New York.
A cikin jawabinsa, babban sakataren ya ce, tsarin "kungiyar G77 da kasar Sin" shine ginshiki wajen kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama, kana yana taka muhimmiyar rawa wajen mayar da batun samun ci gaba a muhimmin aikin na MDD.
A cewarsa, a yayin da wasu kasashe suka yi watsi da batun sauyin yanayi, kasashe biyu da suka fi girma bisa tsarin "G77 da kasar Sin" wato Sin da India suna taka muhimmiyar rawa kan batun, hakan ya bada tabbacin kaucewa fuskantar sakamako mai hadari game da matsalar da sauyin yanayi ke iya haifarwa a duniya.
A sa'i guda kuma, babban sakataren ya nuna yabo kan muhimmiyar rawar da yake takawa a fannonin bakin haura da yin kwaskwarimar MDD. (Bilkisu)