in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin G7 ya bayar da hadaddiyar sanarwa game da yaki da ta'addanci
2017-05-27 12:53:05 cri
Shugabannin da suka halarci taron koli na kungiyar G7 da aka shirya a garin Taormina na kasar Italiya, sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka alkawarta daukar tsaurarran matakan yaki da ta'addanci.

Bisa sanarwar da suka fitar a Jiya Juma'a, yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi muhimman ayyuka ne da suka sha gaban komai, don haka, kasashen bakwai za su gudanar da bincike tare da shigar da karar 'yan ta'adda da masu goya musu baya a gaban kuliya, ta yadda karfin yaki da ta'addanci zai kai wani sabon matsayi.

Baya ga haka, shugabannin kungiyar ta G7, sun lashi takobin murkushe ayyukan ta'addanci da ake gudanarwa a kafar intanet, da hana 'yan tada kayar baya na ketare fita daga yankunan dake fama da rikici zuwa wasu, tare kuma da katse hanyoyin samar da kudi na gudanar da ayyukan ta'addancin.

An bude taron kolin na yini 2 ne a jiya Juma'a, kuma shugabanni daga kasashen 7, da suka hada da Amurka, Jamus, Burtaniya, Faransa, Italiya, Canada da kuma Japan sun halarci taron, inda aka sanya batun tsaro da yaki da ta'addanci a matsayin muhimmin batu da aka tattauna a kai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China