in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wu Haitao: Kungiyar G77 da Sin za su sa kaimi ga samun ci gaba tare
2017-01-14 13:59:29 cri
A jiya Jumma'a 13 ga wata ne, mataimakin wakilin Sin na dindin-din a MDD Wu Haitao, ya bayyana a wajen bikin mika mulkin ga sabon shugaban kungiyar G77 cewa, kungiyar G77 da kasar Sin, za su ci gaba da hada kansu domin samun ci gaba da kiyaye moriyarsu ta bai daya.

A jiyan ne aka gudanar da bikin mika mulkin ga shugaban kungiyar G77 a hedkwatar MDD dake birnin New York, inda kasar Ecuador za ta maye gurbin kasar Thailand wajen shugabantar kungiyar a bana wato shekarar 2017.

Yayin bikin, Wu Haitao ya bayyana cewa, kungiyar G77 da Sin za su ci gaba da kokari tare, domin kyautata aikin kulawa da tattalin arzikin duniya, da tabbatar da aiwatar da shirin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030.

Ban da haka, Wu ya jaddada cewa, bana Sin za ta nuna goyon baya ga aikin Ecuador, shugabar kungiyar G77 a wannan karo, tare da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, da ba da kariya ga moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, domin samun bunkasa tare.

An kafa kungiyar G77 ne a shekarar 1964, a matsayin wata kungiyar duniya da ta kunshi kasashe masu tasowa, da nufin zurfafa hadin gwiwa domin sa kaimi ga raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasashe masu tasowa.

Kasar Sin dai ba memba ba ce ta kungiyar, amma ta dade ta nuna goyon baya ga ayyukanta.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China