A yayin taron, Guterres ya jaddada cewa, kungiyar G77 da kasar Sin suna da muhimmanci sosai wajen cimma burin neman dauwamammen ci gaba, da karfafa ra'ayin kasancewar bangarori da dama. A cewarsa, kungiyar ta nuna karfin jagoranci na hadin kai, ta shugabancin hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, kana ta nuna amfanin dangantakar abokantaka ta hadin kai kan fannonin tattara albarkatu da nuna goyon baya.
Baya ga haka, Guterre ya bayyana fatansa na ganin za a ci gaba da karfafa dangantakar abokantaka ta hadin kai a tsakanin MDD da kungiyar G77 da kasar Sin ta fuskar inganta ajandar neman dauwamamman ci gaba. (Bilkisu)