in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kungiyar G77 ta zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin
2016-09-24 17:37:08 cri

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, a matsayinta na wata muhimmiyar kasa mai tasowa, ya kamata kungiyar G77 ta kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin domin tabbatar da yunkurin neman samun dawamammen ci gaba.

Mr. Liu ya ba da jawabi a gun taron ministocin harkokin waje karo na 40 na kungiyar G77 da aka yi a wannan rana a hedkwatar MDD cewa, a shekarar bara, kungiyar G77 da kasar Sin sun taka rawar a zo a gani a MDD a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma ciki har da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da inganta musayar ra'ayi tsakanin kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa, wadanda suka kiyaye moriyar kasashe masu tasowa yadda ya kamata.

Bugu da kari, Mr. Liu ya bayyana cewa, a kwanan baya, an cimma nasarar gudanar da taron shugabannin kasashen G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin, inda aka samu sakamako a fannoni da dama. Neman samun bunkasuwa shi ne babban jigo na wannan taro. A gun taron, karo na farko da aka mai da aikin neman samun bunkasuwa a wani matsayi mafi muhimmanci, kuma a karon farko ne aka tsara shirin tabbatar da neman samun dawamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030, kana karon farko ne da aka tsai da kudurin ba da taimako ga kasashen Afrika da kuma kasashe maras ci gaba wajen bunkasa masana'antu, wadannan matakai sun kafa sabon tarihi a kungiyar G20, kuma hakan ya samu jinjinawa sosai daga kasashen duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China