in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta fara fitar da albarkatun mai a watan Disamba
2018-05-31 10:18:11 cri
Gwamnatin Kenya ta sanar da cewa za ta fara sayar da man fetur a kasuwannin duniya a watan Disamba da zarar an kammala shirye shiryen farko na fitar da man a mako mai zuwa.

Andrew Kamau, babban sakatare a ma'aikatar man kasar, ya fadawa 'yan jaridu a Nairobi cewa, za'a dinga daukar gangar danyen mai 2,000 a kowace rana daga wajen hakar man dake Lokichar Basin a arewa maso yammacin Kenya zuwa tashar ruwan Mombasa.

Kamau ya ce "Da zarar mun tara adadin man da ya kai ganga 400,000 wanda muke sa ran samu zuwa watan Disamba, to za mu sayar da shi a kasuwannin duniya ta hanyar bin tsarin neman kwangila".

Kasar ta gabashin Afrika ta fara aikin hako man fetur ne a shekarar 2012, kuma kawo yanzu, ta tabbatar da gano kimanin gangar mai 750. A halin yanzu Kenya tana aikin gwaji na farko kafin ta gudanar da cikakken aikin hako danyen man a shekarar 2021. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China