in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Kenya sun ce kasar Sin ita ce abokiyar mu'amala ta hakika wajen cimma muradun Afrika
2018-06-03 16:18:24 cri
Masanan kasar Kenya sun bayyana cewa, tsarin kasar Sin na huldar cin moriyar juna tsakanin kasa da kasa da girmama tsarin siyasar sauran kasashen duniya zai iya zama wani babban ginshikin samar da cigaba, da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Afrika.

Masanan sun bayyana hakan ne a lokacin halartar taron dandali Wanshou karo na 20 wanda aka gudanar a Nairobi, sun ce kasar Sin za ta cigaba da zama babbar jagora wajen tabbatar da muradun da kasashen Afrika ke da su na samar da kayayyakin more rayuwar jama'a irin na zamani, da yaki da fatara da kuma bunkasa cigaban masana'antu.

Peter Kagwanja, babban jami'in gudanarwar cibiyar tsara dabarun cigaban Afrika dake Nairobi, ya ce kasashen Afrika suna daukar kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hulda domin cimma muradun raya cigaban nahiyar Afrika, da samun zaman lafiya.

Kagwanja ya ce, burin da kasar Sin ke da shi ya yi dai dai da ajandar nan ta raya cigaban Afrika nan da shekarar 2063 da kuma samar da zaman lafiya da bunkasuwar nahiyar baki daya.

Sama da masana 50 ne na kasashen Kenya da Sin suka halarci dandalin na Wanshou wanda aka yi wa taken bude tsarin hadin gwiwar Sin da Afrika a sabon zamani karkashin inuwar hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a dandalin sun hada da gina cigaban al'ummomin Sin da Afrika da yin musayar cigaba ta hanyar fadada shawarar ziri daya hanya daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China