in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar jakadar Sin ta jaddada aniyar zurfafa dangantaka tsakanin Sin da Kenya
2018-06-06 11:10:53 cri

Sun Baohong, sabuwar jakadar kasar Sin a Kenya ta sha alwashin yin amfani da sabon mukamin da aka ba ta wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Kenya, da nufin zurfafa mu'amala, da kuma karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Sun, wacce ita ce mace ta farko da aka nada a matsayin jakadar kasar Sin a Nairobi, ta bayyana hakan ne a lokacin da ta mika takardar kama aiki ga shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a birnin Nairobi, kamar yadda fadar shugaban kasar ta Kenyan ta sanar.

A sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar bayan kammala bikin kama aikin sabuwar jakadar a Nairobi, sanarwar ta ce, kasashen Sin da Kenya sun shafe shekaru masu yawa suna cin moriyar mu'amalar dake tsakaninsu a fannoni da dama da suka hada da cigaban fannin samar da kayayyakin more rayuwa da bangaren masana'antu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China