Kwamishinan yankin Garissa Joshua Chepchieng ya tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne da karfe 8 na safe agogon wurin. Ya ce, jami'an da lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ce ta zuwa iyakar Liboi a lokacin da motar da suke ciki ta taka wata nakiya da aka binne.(Ibrahim)