in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan ci rani 186 sun koma gida daga Libya bisa radin kansu
2018-06-08 09:49:34 cri

Hukumar kula da kaura ta duniya IOM dake aiki a kasar Libya ta ce, ta mayar da 'yan ci rani 171 'yan asalin kasar Nijeriya zuwa gida, a wani bangare na shirin hukumar na mayar da 'yan ci rani gida.

Hukumar ta ce, 'yan Nijeriya 171 ne suka koma gida a kashin farko na aikin hukumar na mayar da wadanda suka nemi komawa gida daga Zintan na Libya.

Cibiyoyin kula da masu shige da fice a Libya na cike makil da 'yan ci rani, inda hukumomin a kasar suka yi kira ga hukumomin kasa da kasa su kara taimakawa wajen inganta yanayin rayuwa a cibiyoyin.

Shirin na IOM na ba da damar komawa gida ga 'yan ci rani masu watangarari a Libya. Shirin ya taimaka wa 'yan ci rani 20,000 dake Libya komawa gida a cikin shekarar da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China