Kakakin UNSMIL Sawsan Ghosha, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rahotannin dake nuna cewar 'yan bindigar sun rufe helkwatarta ba gaskiya ba ne.
Kafafen yada labarai na cikin gidan kasar sun rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun rufe helkwatar MDDr har ma sun hana jami'anta shiga ofisoshinsu.
Haka zalika, kafafen yada labaran sun wallafa wasu hotunan motocin 'yan bindigar da suka girke a kusa da helkwatar MDDr.
Helkwatar ta UNSMIL tana garin Janzour, wanda ke da tazarar kilomita 15 daga Tripoli babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)