Wata sanarwa da kafar yada labaran kungiyar IS ta A'maq ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, wasu sojojin daular sun kai samame da makamai daban-daban, kan wani ofishin 'yan sanda da sanyin safiyar jiya a yankin Al-Gannan dake kudancin Ajadabiya, inda suka yi bata kashi da dakarun Janar Haftar.
'sojojin daula' ita ce kalmar da kungiyar IS ke amfani da ita wajen kiran mayakanta da suka kai harin ta'addanci.
Hukumar tsaron Ajadabiya, ba ta bayyana adadin wadanda harin ya rutsa da su daga cikin jami'anta ba. Amma kungiyar IS, ta tabbatar da cewa, an kashe wani adadi na jami'an tsaro tare da kona motoci yayin harin. (Fa'iza Msutapha)