Wasu 'yan kunar bakin wake ne dai suka kutsa kai cikin harabar hukumar zaben kasar da sanyin safiyar Larabar nan, inda bayan musayar wuta da masu tsaron ofishin, sai suka tada wasu bama bamai dake jikin su, wanda hakan ya sabbaba rasuwar mutane da dama, tare da jikkata wasu.
Wannan hari dai na zuwa ne, yayin da gwamnatin kasar mai samun goyon bayan MDD, ke hadin gwiwa da tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, wajen shirya zaben shugaban kasa da na 'yan majalissu, kafin nan da karshen wannan shekara ta bana, kamar da yadda shugaban tawagar, Ghassan Salame ya bada shawarar aiwatarwa.