Jiya Litinin, sojojin ruwa na kasar Libya sun ceto wasu bakin haure su 120 daga bakin tekun kasar daura da birnin Garrabulli, mai nisan kilomita kimamin 55 da Tripoli, babban birnin kasar.
Kwamandan sojojin ruwan Milad Abdalkarim ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, inda ya bayyana cewa an ceci wadannan bakin haure ne 'yan kasashen Afirka daban daban daga tekun da ke da nisan mil 50 daga gabar birnin Garrabulli. Ya kuma kara da cewa, an riga an kai su sansanin sojojin ruwa na Tripoli.
Kakakin sojojin ruwan kasar ya bayyana a Lahadin da ta gabata cewa, an riga an samu gawawwakin wasu bakin hauren su 11, sa'an nan an ceto wasu 283 daga tekun kasar bisa matakai daban daban da aka dauka.
Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, cikin watannin 3 na farkon wannan shekara, an riga an ceto bakin haure fiye da 400 daga bakin tekun kasar ta Libya.(Kande Gao)