in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron sake gina birnin Benghazi na Libya
2018-05-06 16:16:52 cri

An bude taron kasa da kasa, kan sake gina birnin Benghazi na Libya a jiya Asabar, inda ya samu halartar 'yan kasuwa da masana harkokin tattalin arziki daga kasashen 14.

A cewar dan majalisa mai wakiltar yankin gabashin kasar, Mohammed Abdullah, an fara taron ne domin tattaunawa kan sake gina birnin, bayan an shafe shekaru ana yaki da ta'addanci, ya na mai cewa lokaci ya yi da ya kamata a kawar da burbushin barnar da aka yi.

Mohammed Abdullah, ya ce taron ya samu halartar kasashen Larabawa da sauran wasu kasashe 14, inda ya ce zai ba 'yan kasuwa da masu zuba jari damar tattauna damammakin sake gina birnin ta hanyar inganta kayayyakin more rayuwa, yana kuma mai tabbatar da taron ya samu goyon bayan majalisar dokokin kasar da wasu 'yan kasuwar birnin.

Ya kara da cewa, taron zai kai har karshen wannan mako, ya na mai jaddada fatan cimma nasarar taron, domin ya na bayyana burin kowa game da muhimmanci fara aikin farfado da Benghazi domin inganta yanayin rayuwar al'umma.

Har ila yau, dan majalisar ya ce an dage taron nune-nunen sake ginin birnin ne domin ba kasashen waje masu yawa, damar shiga da kuma ganin abubuwan da kamfanoni za su gabatar game da sake ginin birnin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China