Cikin wata sanarwa da ta fitar, Gwamnatin hadin kan kasar, ta yi Allah wadai da harin da aka kai titin Jamal Abdannaser na Benghazi a jiya Alhamis. Inda da ta ce babu abun da zai yi, face sa al'ummar kasar kara jajircewa wajen yaki da ta'addanci.
Ita ma Majalisar wakilan kasar dake da zama a yankin, ta yi tir da harin, ta na mai kira ga hukumomin tsaron kasar, su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, na nemo wadanda ke da hannu tare da hukunta su.
Benghazi wanda shi ne birni na 2 mafi girma a Libya, ya sha fuskantar hare-haren cikin mota da kuma na kunar bakin wake.
A wani mataki na tunkarar tabarbarewar tsaro ne birnin ya kafa wata rundunar hadin gwiwa da ta kunshi sojoji da 'yan sanda.
A bara ne kuma, rundunar soji dake yankin, karkashin Janar Khalifa Haftar, ta samu damar kwace iko da Benghazi, bayan shafe sama da shekaru 3 ta na gwabzawa da kungiyoyin 'yan ta'adda a birnin. (Fa'iza Mustapha)