Wang Yi, wanda ke halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS, ya bayyana hakan yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa game da taron koli na Beijing na FOCAC dake tafe cikin watan Satumbar bana. Ya ce a matsayinsa na dandalin tattaunawa da bunkasa hadin kai tsakanin Sin da nahiyar Afirka, taron FOCAC ya zamo wani jigo na raya kasashe masu tasowa, kuma wata alama dake haskaka tasirin hadin gwiwar sauran sassan duniya da nahiyar ta Afirka.
Jami'in na Sin ya ce cikin shekaru 6 da suka gabata, Sin da Afirka ta Kudu na hadin gwiwar karbar bakuncin wannan dandali, kuma Sin da kasashen Afirka sun kara kaimi wajen bunkasa nasarar dandalin, ta yadda zai ba da damar karfafa hadin gwiwa, da cudanya tsakanin Sin da nahiyar Afirka.
Kaza lika an kammala dukkanin ayyuka da suka shafi gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ke yi wa jagororin Afirka, domin su halarci taron koli na birnin Beijing. Yawancin shugabannin Afirka sun tabbatar da halartarsu a taron kolin. (Saminu)