Ma Zhaoxu, ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron kwamitin sulhun MDDr game da batun zaman lafiya da tsaron tafkin Chadi dake nahiyar Afrika.
Ya bukaci kasa da kasa da su goyi bayan Afrika a kokarinta na yaki da ayyukan ta'addanci.
Mr. Ma ya shedawa kwamitin tsaron MDDr cewa, kamata ya yi MDDr da kasa da kasa su samar da tallafi wanda ya kunshi na fasahar zamani, da bada horo, da kayayyakin aiki, da kuma kudaden gudanarwa a matsayin wani babban taimako da zai tabbatar da tsaro da zaman lafiyar nahiyar ta Afrika.
Haka zalika ya bukaci kasa da kasa su dakile abubuwan dake haddasa matsalolin tashe tashen hankula a Afrika, inda ya yi kira da a kyautata yanayin zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasashen na Afrika, ciki har da batun tafkin Chadi, domin kawo karshen tashin hankali da tsattsauran ra'ayi.
Ma Zhaoxu, ya bada tabbacin cewa kasar Sin a shirye take ta tallafa wa nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)