A kwanakin baya, wasu jami'an siyasa na kasashen yammacin duniya sun zargi Sin wai cewa ta sassauci ikon mallakar kasashen Afrirka da kara yawan basusukan da kasashen Afirka suka ci ta hanyar hadin gwiwar dake tsakaninsu. Game da wannan zargi ne, mataimakin manajan kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin kuma manajan sashen kamfanin dake kasar Kenya Li Qiang ya yi amfani da misalin layin dogo dake tsakanin Mombasa da Nairobi don mayar da martani. Mr Li ya bayyana cewa, an gina wannan layin dogo bisa halin da ake ciki a kasar Kenya, wato an yi bincike da tsara shirin gina layin bisa bukatun kasar Kenya. Ya ce kamfaninsa da gwamnatin kasar Kenya da ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar, da hukumar kula da hanyoyin jiragen kasa ta kasar sun maida hankali ga alfanun da aikin zai haifar a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
Layin dogo dake tsakanin Mombasa da Nairobi aiki ne da ya bude kafa ga tsarin hanyoyin jiragen kasa na gabashin Afirka, wanda ya kawo moriya ga kasashen gabashin Afirka da ba su yi makwabtaka da teku ba, wadanda suke shiga ko fitar da kayayyaki ta tashar tekun Mombasa, da rage kudin da ake kashewa kan jigilar kayayyaki a kasar Kenya har ma ga dukkan yankin gabashin Afirka. Li Qiang ya bayyana cewa, wannan aiki zai sa kaimi ga yunkurin samar da ci gaba na bai daya ga gabashin Afirka, kuma zai kawo sauki ga jigilar mutane da kayayyaki da sadarwa, da kuma moriya ga kasar Kenya har ma da gabashin Afirka, kana alama ce ta zumunta tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)