in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga Swaziland ta shiga cikin kawancenta da kasashen Afirka
2018-06-02 16:14:33 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin ta na kira ga kasar Swaziland ta shiga cikin kawancen Sin da kasashen Afirka cikin hanzari.

Hua Chunying, ta bayyana haka ne yayin wani taron manema labaru da ya gudana jiya a nan birnin Beijing.

Swaziland, ita ce kasar Afirka daya tilo dake hulda da yankin Taiwan. Game da wannan batu ne kuma, Madam Hua ta bayyana cewa, manufar kasar Sin daya tak, ka'ida ce da kasa da kasa suka amincewa, kana kasashe da dama suna raya dangantakar abota ta hadin gwiwa da kasar Sin a dukkan fannoni tare da samun nasarori, shi ya sa take kira ga Swaziland ta shiga cikin kawancenta da kasashen Afirka cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China