in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron dandalin hadin gwiwar gwamnatocin kananan hukumomin Sin da Afirka
2018-05-08 19:59:03 cri

A yau Talata, aka kaddamar da taron dandalin hadin gwiwar gwamnatocin kananan hukumomin Sin da na kasashen Afirka karo na 3 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin, inda mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya halarci bikin kaddamar da taron ya kuma gabatar da jawabi.

A cewar babban jami'in kasar ta Sin, kasarsa za ta tsaya kan manufar bude kofa ga kasashen waje don amfanar kowa, haka kuma kasar Sin na son yin amfani da ci gaban tattalin arzikinta, wajen taimakawa ci gaban nahiyar Afirka. Jami'in ya kara da cewa, yadda gwamnatocin kananan hukumomin bangarorin 2 suke musayar ra'ayi bisa taken "Kau da talauci da samun ci gaba mai dorewa", karkashin inuwar tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, zai taimakawa wajen karfafa huldar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka mai nasaba da manya tsare tsare.

Ban da haka, mista Wang ya gana da firaministan kasar Nijar Brigi Rafini, wanda ya zo kasar Sin musamman ma domin halartar wannan taro.

Yayin ganawarsu, mista Wang ya ce, karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen 2, da neman samun ci gaba tare, buri ne na bai daya na kasashen 2. Kana idan an nazarci ayyukan da aka yi a shekarun baya, za a ga irin ci gaba sosai da aka cimma a fannin hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2.

Ya ce a nata bangare, kasar Sin na son ciyar da huldar dake tsakaninta da Nijar gaba.

A nashi bangaren, firaministan kasar Nijar, Brigi Rafini, ya ce kasar na godiya ga kasar Sin bisa tallafin da ta baiwa Nijar. Sa'an nan ta jinjinawa Sin din game da irin ci gaban da ta samu. Jami'in ya ce kasar Nijar na farin cikin ganin yadda kasar Sin ke taka rawar gani a yayin da ake kula da harkokin duniya, sa'an nan kasar na son koyi daga fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China