A cikin jawabinsa, Wang Yi, ya yi nuni da cewa, a matsayinta na muhimmin dandalin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta fuskar tattalin arziki, an dora wa kungiyar G20 alhakin kara bai wa kasashe masu tasowa zarafi, ta hanyar sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma kara ba su goyon baya ta hanyar inganta hadin gwiwar duniya ta fuskar bunkasuwa.
Ministan harkokin wajen na kasar Sin, ya kara da cewa, za a ci gaba da goyon bayan bunkasar kasashen Afirka. A yayin taron koli na Hangzhou da na Hamburg, an tsai da kudurin goyon bayan raya masana'antu da kara zuba jari a kasashen Afirka da kasashe mafiya rashin ci gaba. Sannan, za a ci gaba da goyon bayan ci gaban Afirka bisa tanade-tanaden da ke cikin "ajandar kungiyar Tarayyar Afirka ta shekarar 2063" kuma bisa ka'idojin "kasashen Afirka ne suka gabatar da bukatunsu, suka kuma amince da shirin da aka gabatar musu, sa'an nan an gudanar da ayyuka masu ruwa da tsaki, karkashin shugabancin Afirka". (Tasallah Yuan)