Yayin taron, Yi Gang ya karfafawa hukumomi masu zaman kansu gwiwar su zuba jari da kasuwanci a nahiyar Afirka. La'akari da yadda aikin zuba jari a nahiyar Afirka ke daukar lokaci tare da fuskantar hadari, ya ba da shawarar yin amfani da tsari mai dorewa na hada-hadar kudi da zuba jari. Bankin jama'ar kasar Sin da bankin raya kasashen Afirka sun kafa asusun raya nahiyar Afirka tare, inda yawan kudinsa ya kai dala biliyan 2 a shekarar 2014, wanda kuma ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ya zuwa yanzu. Asusun raya Sin da Afirka da bankin raya kasa da kasa ya kafa, shi ma ya samar da goyon baya a fannin harkokin kudi ga kasashen Afirka. Wadannan asusu sun yi amfani da albarkatun yankin dake cikin asusun wajen tabbatar da zuba jari da tattara kudi mai dorewa. (Zainab)