in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IAEA ta shirya duba shirin nukiliyar Koriya ta Arewa
2018-06-05 09:38:22 cri

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA a takaice, ta ce a shirye take ta duba shirin raya makamashin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa, muddin dai an ba ta damar taka rawar da ta kamata a lamarin, bayan cimma matsaya a siyasance.

Daraktan hukumar ta IAEA Yukiya Amano, ya shaida wa manema labarai cewa, tawagar hukumar za ta gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, amma wajibi ne hakan ya gudana, bayan cimma matsaya a siyasance tsakanin dukkanin sassan dake da ruwa da tsaki a sha'anin.

Mr. Amano ya kara da cewa, idan har aka kai ga cimma yarjejeniya, IAEA za ta iya samun damar duba sassan da Koriya ta Arewan ke amfani da su wajen ayyukan sarrafa nukiliya domin tantancewa. Ya ce tawagar ma'aikatan hukumar na iya isa kasar cikin 'yan makwanni, da zarar an ba ta damar yin hakan.

Koriya ta Arewa dai ta tarwatsa wurin gwajin makaman ta na nukiliya dake Punggye Ri a watan da ya gabata, a gaban 'yan jaridu na kasashen duniya. Hakan kuma na zuwa ne a yayin da shugaban Amurka Donald Trump, da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ke shirin ganawa da juna a ranar 12 ga watan nan na Yuni a kasar Singapore. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China