in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping, da Kim Jong Un sun zanta a birnin Dalian
2018-05-08 19:48:04 cri

Shugaban kwamitin koli na JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban kasar Koriya ta arewa, kuma shugaban jam'iyyar WPK Kim Jong Un a birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, tsakanin ranekun 7 da 8 ga watan nan na Mayu.

Shugaba Xi ya yabawa shugaba Kim bisa sake zuwa kasar Sin da ya yi bayan kwanaki 40. Shugaba Xi ya ce ziyarar na zuwa ne a wani lokaci mai muhimmanci da ake fuskantar sauye sauye masu sarkakiya a zirin koriya. Ya ce ziyarar ta nuna irin muhimmanci da shugaba Kim ke dorawa game da alakar kasar sa da Sin, da ma tasirin zantawa tsakanin sassan biyu, lamarin da shugaban na Sin ya ce na da ma'anar gaske.

Xi ya kara da cewa, a shirye yake ya sake ganawa da Kim a nan gaba, domin ci gaba da tattauna matakan samar da zaman lafiya da lumana, tare da bunkasar alakar Sin da Koriya ta arewa. Har wa yau ya yi fatan sassan biyu za su cimma nasarar wanzar da yanayin zaman lafiya mai dorewa a zirin koriya, da yankin da suke, da kuma samar da ci gaba da walwala.

Ya ce zai yi aiki tare da shugaba Kim, wajen saita alkiblar dukkanin hukumomi masu ruwa da tsaki na kasashen biyu, ta yadda za su samar da ci gaban alakar kasashen, da cimma gajiyar su da ta al'ummun su, tare da ba da karin gudummawar samar da zaman lafiya da lumana a yankin da suke.

A nasa bangare, shugaba Kim ya ce kasar sa da Sin abokan juna ne, kuma yanayin da zirin koriya ke ciki ya shiga sabon yanayi na samun ci gaba, tun daga watan Maris din shekarar bana.

Shugaba Kim ya ce ya sake zuwa kasar Sin ne a wannan karo, domin bayyanawa Shugaba Xi halin da ake ciki, da fatan karfafa yanayin tattaunawa da hadin gwiwa da kawance tsakanin kasashen biyu. A daya hannun kuma, yana fatan hakan zai bunkasa zaman lafiya da daidaito a yankin da suke.

Game da yanayin da ake ciki a zirin koriya, shugaba Xi ya ce, da hadin gwiwar dukkanin sassa da batun ya shafa, ana samun ci gaba matuka wajen dakile zaman dar dar a zirin, matakin da zai kai ga warware takaddamar yankin ta hanyar siyasa.

Ya ce Sin na jinjanawa Koriya ta arewa, bisa manufarta ta goyon bayan kawar da makaman nukiliya daga zirin, da kuma fatan ci gaba da tattaunawa tsakanin Koriya ta arewa da Amurka, game da kaiwa ga warware matsalolin zirin koriyar baki daya.

Shi kuwa shugaba Kim bayyana godiyarsa ya yi ga kasar Sin, bisa tsawon lokaci da ta shafe tana baiwa wannan manufa ta kawar da makaman nukiliya daga zirin koriya goyon baya. Baya ga aniyarta ta ganin an samu cikakken yanayin zaman lafiya da lumana a yankin baki daya. Ya ce kasar sa na nuna cikakken goyon baya ga wannan manufa. Daga nan sai ya bayyana fatan ganin dukkanin sassan da wannan batu ya shafa, sun yi watsi da matakan nuna karfin tuwo, da barazanar tsaro kan kasar sa, duba da cewa, ba wata bukata da za ta tilasawa kasar sa samar da makaman nukiliya, kuma cimma yanayin kawar da irin wadannan makamai daga yankin na zirin koriya abu ne mai yiwuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China