in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin
2018-05-03 20:37:46 cri
Yau Alhamis, shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, wanda a yanzu haka yake ziyara kasar.

Wang ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa ga Kim Jong Un, inda ya ce, a kwanakin baya ne, Kim ya ziyarci kasar Sin, inda ya yi ganawa mai ma'anar tarihi tare da shugaba Xi, da cimma matsaya daya kan wasu muhimman fannoni, da bude wani sabon babi ga ci gaban huldodin kasashen biyu.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin ta taya shugabannin Koriya ta Arewa da ta Kudu murnar ganawa da juna cikin nasara, abun da ya samar da babban zarafi ga daidaita batun zirin Koriya a siyasance. Ya ce kasar Sin na goyon-bayan Koriya ta Arewa wajen habaka tattalin arzikinta, da kawar da makaman nukiliyarta.

A nasa bangaren, Kim Jong Un ya ce, kasarsa na fatan yin kokari tare da kasar Sin, wajen kara raya dangantakar kasashen biyu. Kim ya ce, kawar da makaman nukiliya baki daya daga zirin Koriya, babban matsayi ne da Koriya ta Arewa ke tsayawa a kai. Koriya ta Arewa na fatan farfado da shawarwari, da kara samun fahimtar juna tsakanin bangarorin masu ruwa da tsaki. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China