in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koyon Sinanci: jinkirta / Watakila za a jinkirta ganawa tsakanin shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa
2018-05-24 15:26:52 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in sun kira taron manema labaru a ranar Talata data gabata, inda shugaba Trump ya ce watakila za a jinkirta ganawar da ake shirin gudanarwa tsakaninsa da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Haka zalika, shugaban kasar Amurka ya ce, kasarsa ta gindaya sharadin ganawar. Idan an ki biya bukatun kasar Amurka, to, ba za a yi ganawar ba.

Bari mu duba tsohon bakaken Sinanci dake da ma'anar "jinkirta". Ma'anarsa ta tushe ita ce wani fursuna yana tafiya sannu a hankali sakamakon yadda aka dinga bugunsa da sanda.

Maganar da shugaba Trump ya yi, ta sheda mana wanene ke "bugun mutum da sanda", wato matsawa wani mutum lamba, lamari ne da ya sa aka jinkirta ganawar da ake shirin yi tsakanin shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa.

Mataimakin ministan harkokin waje na farko na Koriya ta arewa Kim Kye Gwan ya bayyana a ran 16 ga wata cewa, Amurka na yunkurin kaskantar da Koriya ta arewa ta hanyar kawar da gwamnatin kasar, kamar yadda ta yi a Libya da Iraki.

An shawarci Donald Trump cewa, idan har yana da lokaci, sai ya raka jikarsa su koyi Sinanci tare, matakin da zai zurfafa dangantakarsu, har ma zai wayar musu da kai ta yadda za su fahimci haruffan Sinanci.

Watakila ba za a bukatar jinkirta ganawa tsakanin shugabannin biyu ba, sai dai idan Amurka ce ta yi watsi da sharudan da ta sakawa Koriya ta arewa, ta kuma bi hanyar da Sin take tsarawa don ganin an kawar da makaman nukiliya da ma kafa tsarin tabbatar da zaman lafiya a zirin na Koriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China