Jiya Alhamis, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da soke shawarwarin da zai yi da takwaransa na Koriya ta Arewa a ranar 12 ga watan Yulin bana a kasar Singapore. A jiya ne kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa, Kim Kye-gwan ya bayyana cewa, kasarsa na son komawa teburin shawarwari da kasar Amurka a kowa ne lokaci kuma ta hanyar da ta dace.
Game da wannan batu, Lu Kang ya ce, kasar Sin na fatan bangarorin biyu za su kara nuna juriya da hada kai tare, don ci gaba da warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari.
Har wa yau, Lu ya ce, kasar Sin na maraba da matakin da Koriya ta Arewa ta dauka, na lalata cibiyar gwajin makaman nukiliya na Punggye-ri.(Murtala Zhang)