Mr Pompeo ya bayyana a wannan rana cewa, idan Koriya ta Arewa ta yi watsi da makaman nukiliyarta, kasar Amurka za ta soke takunkumi da aka kakabawa kasar Koriya ta Arewa tare da taimake ta wajen samun wadata.
Pompeo ya yi nuni da cewa, kasar Amurka za ta taimakawa kasar Koriya ta Arewa a fannonin makamashi, wutar lantarki, kayayyakin more rayuwar yau da kullum, aikin gona da sauransu. Kana ya jaddada cewa, sharadin da aka saka kan wannan batu shi ne kawar da makaman nukiliya a dukkan fannoni a zirin Koriya. (Zainab)