Ganawar dake tsakanin shugabannin Sin da Koriya ta Arewa ta taimakawa raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata
Shugaban kwamitin koli na JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban kasar Koriya ta arewa, kuma shugaban jam'iyyar WPK Kim Jong Un a birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, tsakanin ranekun 7 da 8 ga watan nan na Mayu. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau 9 ga wata cewa, yanzu haka an shiga muhimmin lokacin samun canji a zirin Koriya, shugabannin kasashen Sin da Koriya ta Arewa sun yi mu'amala bisa manyan tsare-tsare, wanda ya sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, da taimakawa wajen cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da samun zaman lafiya mai dorewa a zirin. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku