in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce samun zaman lafiya na bukatar kyakkyawan kudurin shugabanci da karfin gwiwa daga dukkan bangarori
2018-05-18 13:41:51 cri

Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina J. Mohammed, ta ce samun zaman lafiya ya dogara ne da kyakkyawan kudurin shugabanci da kwarin gwiwa daga dukkan bangarori.

Da take jawabi ga taron MDD kan batun Falasdinu, Amina Mohammed, ta ce dole ne al'ummomin kasashen waje su yi aiki tare wajen samo mafitar da mutunci zai ta maye gurbin tsoro, sannan adalci ya ce maye gurbin danniya.

Ta ce yayin da ake bikin cika shekaru 70 da samar da daftarin da ya ayyana hakkokin dan Adam, kamata ya yi ka'idojin dake kunshe cikin daftarin su nuna hanyar da ya kamata a bi, wajen binciken mafita mai dorewa ga batun Falasdinu, mafitar da za ta dogora da dokokin kasa da kasa da halattaccen muradun Falasdinawa da Yahudawa, domin samu maslaha da sanin nauyin da ya rataya kan kowa.

Da take tsokaci game da rikicin Gaza na baya-bayan nan, Mataimakiyar Sakatare Janar din ta jadadda bukatar daukar mataki.

Ta yi alkawarin cewa, MDD za ta ci gaba da mara baya ga Falasdinawa da Yahudawa a kan tafarkin neman zaman lafiya, ta hanyar taimaka musu daukar gagarumin matakin samun mafita, ta samun kasashe biyu, makwabta dake zaune cikin kwanciyar hankali, kuma cikin iyakokin da aka amince da su, da kuma Kudus a matsayin babban birnin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China